Bidiyo Labarai

Zamu kawo karshen Rikicin fulani da manoma a najeriya Cewar Gidauniyar Sir Amadu Bello Sardauna

 

Daga Aliyu Muhammad,kaduna

Gidauniyar Sir Amadu Bello sardauna tayi wani taro na kwana Biyu a kaduna Domin gano musabbabin yawan rikicin Da ake samu tsakanin fulani makiyaya Da manoma a taraiyar najeriya.

Rikicin fulani da manoma dai rikicine da yaki ci yaki chinyewa kuma yana lashe Rayuka da dama masamman a garin Manbila na jahar taraba Dr. Shatima Ají Ali yana cikin jigo a wannan gidauniya ta Sir. Amadu bello sardauna yayiwa manema labarai karin haske da cewa wannan Rikici na fulani da manoma da yake yawan faruwa a wannan kasa ya Damemu kuma dolene mu samu hanyar Da zamu warware wannan Rikici da yake nema ya gagari kundila.

Dr. Shatima Ají Ali yace dolene su kawo Duk bangarorin Biyu domin suji matsalolin su.

Hajiya khadija Haruna Ardido kuwa Dayace daga cikin shuwagaban nin mata ‘yan kungiyar miyatti Allah a najiriya Cewa tayi Rashin barwa fulani labin kiwo shine musabbabin wannan rigima.

Khadija Ardido ta roki gwamnatin taraiya Data sa hannu domin kawo karshin zubar da jinin fulani da barnata dukiyoyin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *