cover
Bidiyo Labarai

Mutanen Hayin Kogi Mashigi A Kaduna Sun koka

Daga Aliyu Muhammad

Jama’ar Hayan kogi mashigi da yake a karamar hukumar igabi ta jahar kaduna A taraiyar Najeriya sun koka dan gane da matsalar rashin hanya da asibiti da kuma makaran ta da suke fama da ita.

Alhaji umar Adamu Dagacin Hayin kogi mashigi ya koka matu ka na matsalar hanya da asibiti da kuma makaran tar yaran su, umar Adamu yace idan mace haihuwa ta zo mata da gardama kafin a fidda ita zuwa asibita dake cikin gari lallai mace tana iya rasa ranta, umar Adamu yayi kira ga Gwamnati da ta kawomusu dauki domin gyara musu makaran tun yaran su da kuma gina musu asibiti a wannan gari nasu.

Malama Bara’atu kuwa mazauni yar garin hayin kogi mashigi tace lallai suna cikin mummunar matsala masamman idan mace tazo haihuwa, sannan suna da karancin ruwan sha sannan makaran tar yaran su ta lalace ta Inda idan damina tayi yaran kara tunsu yana tsayawa daga karshe tayi roko ga gwamnatin jahar kaduna da ta duba halin da suke ciki domin kawo musu dauki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *